IQNA

A Faransa Za A Yi Zama Kan Matasa Musulmi Da Kuma Musulunci

14:19 - November 03, 2009
Lambar Labari: 1844328
Bangaren kasa da kasa:a kasar Faransa ne za a gudanar da wani zama kan matasa musulmi da kuma Musulunci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ce ta nakalto daga Ujm ta watsa rahoton cewa; a gurin wannan taro Hassan Iquioussen hatibin juma'a a masallacin garin Escaudai zai gabatar da jawabi ka lokacin gudanar da wannan taro na matasa musulmi da kuma Musulunci.Har ila yau mahalarta wannan taro za su gabatar da jawabai da makaloli kan dangantakar ma'aikin Allah tsira da aminicin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da matasa.Nauyin day a rataya a wuyan matasa an lamarin day a shafi Musulunci da kuma hanyoyin magance matsalolin da ke addabar matasa a musulmi a duniyarmu ta yau a kasashe daban –daban dab a na Musulunci ba suna daga cikin abubuwa da za a tattauna a gurin wannan zama.

486605

captcha