Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; An bude wani gidan radiyo na kur'ani a karon farko a nahiyar turai, wanda zai rika watsa shirye-shiryensa ta hanyar internet daga kasar Belgium. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gidan radiyo yana shirye-shirye masu kayatarwa na kur'ani mai tsarki domin amfanar mabiya addinin musulunci. 486884