Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar kula da fikihun msulunci cewa; cibiyar ta fitar da bayani ga mahajjatan bana da ke cewa; Ya rataya kan mahajjata da suke gudanar da ayyukan ibadar haji a kasa mai tsarki da su yi aiki da koyarwar addini a cikin dukkanin ayyukansu da za su gudanar na ibada. Bayanin ya ci gaba da cewa gudanar da ayyukan ibadar hajji bisa koyarwar addini shi ne abin da ake bukata domin samun tasirinsa a cikin al'ummar musulmi. 486912