Bangaren Adabi: mawaka hamsin ne za su halarci taron mawaka da za a gudanar a nan Iran a daidai wannan lokaci na tunawa da cika shekaru talati na juyin juya halin Musulunci.
Mustapha Imidi sakataren kula da harkokin shiryua kasuwar baje koli na kasa da kasa na wakar Fajir a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa: komitin shirya wannan kasuwar baje koli karo na hudu ta mawaka ta kasa da kasaya yi zamansa a makon day a gabata inda aka samu halartar ministan da ke kula da al'adu da fadakarwa na Iran inda kuma a gurin wannan ganawa aka gabatar da rahoto kan shirya wannan taro da kasuwar baje kolin wakoki da mawaka na kasa da kasa a daidai wannan lokaci na tunawa da zagayowar cika shekaru talatin na juyin juya halin Musulunci a Iran.
487647