Bangaren manema labarai: Ya zuwa yanzu an tuna da manyan malummai 66 a duniya da ma'aikatar aika sakonni ta Iran ta yi ta hanyar sa hotunansu a kan sarki.
Nadir Daryaban wani mai bincike kan tarihin kan sarki a Iran a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna kan wannan lamari ya bayyana cewa: Iran tana daya daga cikin kasashe na gaba-gaban ta fuskar saurin kawo sauyi a cikin irin kan sarkin da take amfani da su kuma yawanci tana bawa bangare ilimi da girmama malumman addini muhimmanci da kuma yan gwagwarmaya da suka taka rawar gani a duniya.Ya fito fili ya kara da cewa; a cikin wadannan shekaru talatin na nasarar juyin juya halin Musulunci malumman addini satin da shidda ne aka yi amfani da hotunansu a kan sarki.
487635