Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan nakaltowa daga risalehaber ta watsa rahoton cewa: an fara taron share fage na komitin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasashen musulmi kuma a yau ne komitin zai ci gaba da taronsa domin binciken hanyoyin kara fadada hanyoyin binkasa huldar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasashe hamsin da bakwai na kasashen muslmi mambobin a cikin kungiuyar hadin kan kasashen musulmi.Har ila yau a daidai wannan lokacin na tunawa da shekaru arshirin da biyar da kafa wannan komiti za samu halartar shugaban kasar Turkiya Abdallah Gol Da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ikmul Dine Ihsan Uglu.
488448