IQNA

An Kafa Na'urorin Bincike 700 A Falfajiyar Dakin Allah

Bangaren kasa da kasa: Yahya Alzahrani komandan rundunar tsaro a birnin Makka ya bada labarin kafa na'urori dari bakwai a falfajiyar dakin Allah domin lura da tsaro da zirga-zirgar mahajja a bana.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta nasij ta watsa labarain cewa: Yahya Alzahrani komandan rundunar tsaro a birnin Makka ya bada labarin kafa na'urori dari bakwai a falfajiyar dakin Allah domin lura da tsaro da zirga-zirgar mahajja a bana. Ya kuma kara da cewa; burin wannan aiki n akafa na'urori fadada tsaro da kwanciyar hankali a tsakanin falfajiyar da sanin mai shiga da fito da abubuwa da kan kai kawo a falfajiyar domin yin hakan zai bawa mahajjata kariya da cikekken tsaro da kuma jin dadin yin ibadarsu cikin nucuwa da kwaciyar hankali.

488414