IQNA

Wata Cibiya A Kasar Pakistan Ce Ta Lashe kyautar Yaki Da Jahilci A Duniya

Bangaren kasa da kasa; hukumar kula da yada ilimi da al'adu na Musulunci Aisisko ce a jiya ta zabi cibiyar bada horo da ilimi ta kasar Pakistan a matsayin wadda tafi taka rawar gani wajen yaki da jahilci a duniya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Kudus Press ta watsa rahoton cewa: hukumar kula da yada ilimi da al'adu na Musulunci Aisisko ce a jiya ta zabi cibiyar bada horo da ilimi ta kasar Pakistan a matsayin wadda tafi taka rawar gani wajen yaki da jahilci a duniya. Wannan abin jinjinawa ne da kuma yabawa wannan cibiya da irin kokarin da take yin a yada ilimi musamman yaki da jahilci da ke zama daya daga cikinn wannan matsaloli a wannan zamani da ke yi wa rayuwar dan adam barazana da kuma ke kara mayar da shi baya.

488402