IQNA

Komi Ya Kammala Na Fara Zuwa da Shigar MahajjataN Iran A Cikin Makka

Bangaren kasa da kasa: mai kula da dawainiyar mahajjatan Iran ya bayyana cewa komi ya kammala za su fara zuwa birnin Makkah.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce daga birnin Madina ta watsa rahoton cewa: Hasan Sakayi shugaban ofishin wakilin hukumar hajji da Umara ta Iran kuma mai kula da yankin Makkah ya bayyana cewa komi ya kammala wato shirye-shirye sun kammala mahajjata za su fara shiga da zuwa cikin birnin Makkah ba tarecda wata matsala ko fargaba ba.Kuma tuni sun kammala shirye-shirye da likitoci masu kula da lafiyar mahajjata a bana a lokacin ayyukan haji.

488406