Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CERSI cewa; Za a gudanar da wani taron kara wa juna ilimi kan yadda ake gudanar da ayyukan haji a kasar Faransa, wanda cibiyar gudanar da bincike kan musulunci ta kasar za ta dauki nauyin shiryawa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar musulmi da suke da niyar tafiya kasa mai tsarki domin safke farali. 489019