IQNA

Ofishin Da Ke Kula Da Yada Al'adun Iran A Nigeria Ya Jaddada Fadada Dangantaka Da Jami'ar Ansarul Din

Bangaren siyasa da zamantakewa: ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a Nigeria ya jaddada niyarsa ta fadada dangantakarsa da jami'ar ansarul Dine.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa;Azimi Nasaru Abadi mai kula da ofishin yada al'adu Iran a kasar Nigeria a lokacin da yake wata ganawa da Profesa Babatunde Falaviyo Lisiva shugaban wannan jami'a ta Ansarul Dine a wannan kasa ya bayyana masa niyar ofishinsa na fadada dangantakar da ke tsakanin ofishin yada al'adun Iran a Nigeria da kuma wannan jami'a.Kuma a matakin farko na wannan dangantaka za a fita yawan bude ido da daliban wannan makaranta.Kuma ya kara bayyana muhimmanci da yada ilimi a wannan kasa da hanyoyin bi na cimma moriyar hakan.



489580