IQNA

Kasuwar Baje Kolin Kayan Musulunci Da Hijabi Abin Suturta Jiki

Bangaren zamantakewa; a watan Dai ne ofishin da ke kula da jin dadin mata da iyali na lardin Tehran ya shirya kasuwar baje kolin kayan Musulunci da hijabi abin suturta jiki.
Farhinaz mai bawa gwamnan birnin Tehran shawara a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta bayyana cewa: wannan kasuwar baje koli an gudanar da ita ne domin bayyana kayayyakin Musulunci da suturar Musulunci iri –iri da kuma nuna hijabobi suma iri-iri kama daga na yara kanana zuwa manya da saffi.Ta kara da cewa" taken wannan kasuwar baje koli shi ne matan kasata kuma ma'aikatar kula da zamantakewar al'umma ta taimaka wajen ganin an gudanar da wannan kasuwar baje kolin ta kayayyakin sanyawa na mata a musulunce.Kawai lokaci ne ake jira domin bawa duk mai son ganewa idonsa wannan kasuwar baje koli damar zuwa da ganewa idonsa.

489500