Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Ma'a cewa; An gudanar da wani zaman taro a zirin gaza, inda aka girmama wasu mata mahardata kur'ani mai tsarki a yankin. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin ayyukan da cibiyar kula da harkokin kur'ani a Gaza ke gudanarwa, kuma yanzu haka ana ci gaba da karfafa mahardata wajen ci gaba da himma don kiyaye hardarsu. 489344