IQNA

14:57 - November 10, 2009
Lambar Labari: 1847412

An BuGa Wani Littafi Kan Dalilan Mazhabar Imamiyya A Labanon

Bangaren kasa da kasa; An buga wani littafi mai suna bahasi kan dalilai na hankali a wajen mazhabar Imamiyya, wanda aka buga tare da yadawa a kasar Labanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na Irsan Ilyan cewa; An buga wani littafi mai suna bahasi kan dalilai na hankali a wajen mazhabar Imamiyya, wanda aka buga tare da yadawa a kasar Labanon. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafi wanda Muhammad Rushdi ya rubuta ya tabbatar da irin dalilai da mazhabar iyalan gidan manzon Allah ta dogara da su a hankalce wajen bin hukunce-hukunce daiodai da koyarwar manzon Allah. 490050


captcha