Bangaren kasa da kasa; Iran wuri ne na sanin al'adu an gabaci da yammacin duniya, domin kuwa kasa ce da ta hada dukkanin masana da suke da fice ta fuskacin sanin al'adu na yammaci da kuma gabacin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga wani malamin jami'ar Tehran cewa; Iran wuri ne na sanin al'adu an gabaci da yammacin duniya, domin kuwa kasa ce da ta hada dukkanin masana da suke da fice ta fuskacin sanin al'adu na yammaci da kuma gabacin duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan masani wanda ya kwashe tsawon shekaru yana koyarwa a jami'ar Tehran , ya tabbatar da cewa akwai dubbai irinsa da suke iyakacin kokarinsu wajen kara fadakar da dalibai kan irin muhimmancin da ke tatatre da sanin al'adu daban-daban. 491290