Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar da ke kula da shirya tarukan falsafa a Iran cewa; Za a gudanar da wani zama da zai yi dubi kan mahangar falsafa dangane da ilmomi na nazari da kuma ilmomi na aikace, za agudanar da zaman taron ne a matsayi na kasa da kasa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar manyan malaman jami'a daga sassa daban-daban na kasashen duniya. 491307