Dole Manyan Kasashe Su Taka wa Isra'ila Birki Kan Ta'addancinta
Bangaren kasa da kasa; Babban daraktan kungiyar yada ilimi da al'adun Musulunci ta ISESCO ya bayyana cewa, dole ne manyan kasashen duniya da suke da karfin fada a ji su taka wa Isra'ila birki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na kungiyar hadin kan kasashen musulmi cewa; Babban daraktan kungiyar yada ilimi da al'adun Musulunci ta ISESCO ya bayyana cewa, dole ne manyan kasashen duniya da suke da karfin fada a ji su taka wa Isra'ila birki kan ta'addancin da take aikatawa. 491378