Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bnagaren yada labaransa da ke tare da tawagar mahajjata cewa; Sama da mutane 20000 ne daga cikin mutanen kasar saudiyya suke gudanar da hidima ga mahajjatan bana a makka. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin muhimman batutuwa da suka cancanci a yaba da su dangane da yaddamutanen kasar suke sa kansu gudanar da ayyukan hidima ga alhazai da suka zo daga kasashe daban-daban. 491914