IQNA

Wajibcin Bincike Da Nazari Wajen Tafiyar Da Maktaba Ta Tafsiri

Bangaren tunani da ilimi: yin bincike da nazari na taimakawa malamai ta fuskar tafsiri.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga birnin Qum ta watsa rahoton cewa:hujjatul islami Muhammad Ali Riyadi Isfahani malamin jami'a a jami'ar Mustapha (SWA) Al'alami a wani zama a kan littafai da maktaba ta tafsiri da cibiyar da ke kula da ilimi a Hauza ta shirya ya bayyana cewa; ana bukatar a maida hankali da himma fiye da kima wajen bawa bangaren kur'ani da tafsiri da kuma bangaren zurfafa tunani da nazari.

492581