Bangaren kasa da kasa; An fara shirye-shiryen gudanar da wani babban taro na idil Gadir a birnin London na kasar Birtaniya, wanda cibiyar kula da harkokin musulmi za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na IC-EL cewa; An fara shirye-shiryen gudanar da wani babban taro na idil Gadir a birnin London na kasar Birtaniya, wanda cibiyar kula da harkokin musulmi za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa sheikh Ahmad Hanif shi ne zai gabatar da jawabi a wurin taron dangane da wilayar halifancin Imam Ali (AS) Taron dai zai samu halartar bangarori daban-daban na musulmi kasar Birtaniya.492405