IQNA

Za A Gudanar Da Wani Taro Kan Falsafa A Birnin Moscow Na Rasha

Bangaren fikira da ilimi; Za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan ilmin falsafa da mahangar addinai kan wannan ilimi, da kuma tattaunawa kan al'adu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar rasha cewa; Za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan ilmin falsafa da mahangar addinai kan wannan ilimi, da kuma tattaunawa kan al'adu. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suka fi cima mabiya addinai tuwo a kwarya, inda ilimin falsafa ke fayyace boyayyun ilmomi. 492416