Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran kasar Sudan cewa; An gudanar da wani zaman taro kan tsarin hukumar musulunci an Iran da kuma barazanar kasashe masu girman kai a kan Sudan. Bayanin ya ci gaba da cewa wanna taro ya yi dubi ne kan irin darussan da za a iya dauka daga tsarin musulunci da jamhuriyar muslunci ta Iran ke tafiya a kansa, da kuma yin dubi kan barazanar da kasar Sudan ke fuskanta daga kasashe masu girman kai. 492672