Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar musulmin Amurka cewa; An fitar da wata sabuwar fassarar kur'ani mai tsarki a kasar amurka a cikin harshen turanci. Wanda daya daga cikin malaman musulmi an kasar Amurka ya dauki nauyin fassarawa. Bayanin ya ci gaba da cewa Mohammad Asi daya daga cikin jagororin mabiya addinin muslunci na Amurka, kuma babban limamin maasalllacin birnin Washington, shi ne ya fassa kur'anin. 493266