Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga wani shafin internet na wata kafar yada labarai ta Musulunci cewa; Za a gudanar da wani zaman taro kan tarihin addinin Musulunci a yankin gabas ta tsakiya, wanda za a gudanar a birnin London fadar mulkin Birtaniya. Bayanin ya ci gaba da cewa zaman taron zai samu halartar masana daga sassa daban –daban na kasashen turai, domin kara wa juna sani kan hakikanin tarihin muslunci. 514172