Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga wani kamfanin dillancin labarai na Afrika cewa; Majami'ar jahar Florida ta wulakanta kur'ani mai tsarki, bayan da ta sa aka lika wasu hotuna masu nuna cin zarafi ga addinin Musulunci gami da wasu rubuce-rubuce. Bayanin ya ci gaba da cewa babu wata dangantaka tsakanin ayyukan ta'addancin da wasu suke aikatawa da sunan addinin muslunci a fadin duniya. 514968