IQNA

16:23 - December 30, 2009
Lambar Labari: 1866914

Matsayin Jagora Kan Hankoron Kasashe Masu Hankoron Yin Mulkin Mallaka A Yankin

Bangaren kasa da kasa; Matsayin jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran dangane da matakan da kasashe masu girman kai suke dauka na yin sabon mulkin mallaka a kan al'ummomin yankin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; Shugaban bangaren kula da harkokin ilmi da al'adu na jamhuriyar Musulunci a Iran da ke reshen Kuwait Hojj. Abul fadel Razavi Ardukani, ya bayyana cewa an fitar da wasu bayanai kan matsayin jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran dangane da matakan da kasashe masu girman kai suke dauka na yin sabon mulkin mallaka a kan al'ummomin yankin. Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran juyin juya halin ba zai tab ayin saku-saku kan batun kare manufofin jamhuriyar Musulunci, kuma ya jaddada cewa al'ummar Iran ba za su taba mika wuya ga zaluncin kasashe masu girman kai ba.514902


captcha