Bangaren kasa da kasa: za a kafa kungiyar hadin kan malummai musulmi a wani kokari na tabbatar da sulhu da ahadin kai a tsakanin musulmai a Filipine.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Islam Online ta watsa rahoton cewa; kimanin mutane dari biyu daga cikin malumai musulmi a kasar Filipine daga kungiyoyi daban-daban na musulmi a wannan kasa suka halarci gurin zabar mambobin wannan kungiya.Shi kuwa AbdulKheir Tarasan shugaban day a shirya da kula da wannan taro ya bayyana cewa; wannan taro day a dauki nauyi da bin hanyoyin taimakawa musulmi a fadin duniya da kuma hanyoyin samar da hadin kai a tsakanin musulmin.
531797