IQNA

An Bukaci Samar Da Wata Hanyar Internet Da Yaruka Kasashen Musulmi

Bangaren fasaha da al'ada: wadanda suka halarci taron kasa da kasa kan bincike ilimi da binkasarsa a kasashen musulmi a birnin Istambul a bayanin bayan taro sun bayyana muhimmancin samar da kafar Internet a kasashen musulmi.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta na kasar Turkiya ta watsa rahoto bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Aljazira ta bayyana cewa; wannan taro ya yi amfani da zama wata madogara ce ga kasashen musulmi da kuma hanyar da za ta sa irin wadannan kasashe su zauna da gindinsu kuma a duk shekara za ashirya irin wannan taro tare da daukan dawainiyar gudanarwa daga kungiyoyin bincike na kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kuma za a gudanar a birnin na Istambul na kasar Turkiya duk shekara.

532424