Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga kasar Labanon ta watsa rahoton cewa; Ayatullahi Kablan mukaddashin shugaban majalisar koli ta malumman shi'a a Labanon ya bayyana cewa: gwagwarmayar Labanon ce ta rusa lakabin da ake yi wa rundunar sojin HKI dab a a iya cinta a yaki. Har ila yau ya kara da cewa; hadin kai tsakanin al'ummar Labanon da kuma kokari tukuru shi ne zai kara tabbatar da wannan nasara da sauran nasarori a nan gaba.
533108