IQNA

An Bude Zaman Taro Na Makon Al'adun Iran A Ghana

Bangaren al'adu; An bude wani zaman taro na makon al'adun Iran a kasar Ghana, wanda ke samun halartar masana daga jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma kasar ta Ghana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa An bude wani zaman taro na makon al'adun Iran a kasar Ghana, wanda ke samun halartar masana daga jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma kasar ta Ghana. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin shirye-shiryen ma'aikatar kula da harkokin al'adu da ilimi ta kasar Iran a kasashen ketare, da take gudanarwa domin kara karfafa dangantaka ta ilmi da ala'du tsakanin Iran da kuma sauraran kasashen duniya. 534491