Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna bayan ta nakalto daga majiyar larabarai ta gwam,natin Hadeddiyar Daular Larabawa ta watsa rahoton cewa; Umar bin Abdull Aziz Alkasimi sakataren shirye-shirye da tsare-tsare na wannan gasar ta kur'ani mai girma a garin Ra'asul Kheima da kuma ke karkashin mu'assisar Ulumul Kr'ani a wannan gari a wani taron manema labarai ya bayyana cewa; wannan gasar za a gudanar da ita cikin kashi biyu bangaren maza da kuma bangaren mata kuma kimanin mahardata dari da tamanin da takwas ne suka rubuta sunayensu amma daga cikin su dari da bakwai ne za amince su fafata da juna.
535064