Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga yankin Jamhuriyar Azarbeijan ta watsa rahoton cewa: Sheikh ul Islam Allahu Shakur Pashazade shugaban ofishin da ke kula da musulmi a kasar Kafkaz ya yi nuni da barazanar da musulmi ke fuskanta da kutsawar al'adun yammacin turai a cikin lamuransu. Kuma ya fadi haka ne a daidai lokacin tunanwa da cika shekaru talatin da daya da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran.
534640