Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Islam Online da kuma jaridar Airish Tamz da ake bugawa a Irland cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ce ta watsa rahoton cewa; gwamnatin Irland tana kokarin ganin ta fara amfani da tsarin tattalin arziki irin na Musulunci kuma ta mika wannan bukata ga majalisar dokokin kasar. Da dama daga cikin kasashen yammacin Turai sun fara tunanin yadda za su yi aiki da tsarin tattalin arziki irin na Musulunci da hakan zai kare su daga matsalar da tattalin arzikin kasashensu ke fuskanta a yau.
535641