Bangaren siyasa da zamantakewa: a kasar Yunan za a gudanar da bukin tunawa da cika shekaru talatin da daya da nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Mahdi HunarDust jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a Yunan ya bayyana cewa: a kasar Yunan za a gudanar da bukin tunawa da cika shekaru talatin da daya da nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran. Kuma a wannan bukin da ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a wannan kasa za a nuna irin ci gaban da Iran ta samu ta fuskoki daban daban kama daga ilimi ,al'adu,siyasa .ma'anawiya da masana'antu.
535843