Bangaren siyasa da zamantakewa: Allama Said Muhammad Husein Fadllah babban malamin yan shi'a a kasar Labanon a jiya ne ya maida martani kan yadda Amerika ke marawa gwamnatin HKI baya a yake-yaken da mamayan da take yiwa kasashen musulmi da jaddada cewa; musulmi da larabawa suna da karfin da za su sake cin nasara kan gwamnatin mamaye ta HKi.