IQNA

A Bangladesh A Baje Kolin Fasaha Don Tunawa Da Nasarar Juyi

Bangaren fasaha da al'adu: ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a Bangladesh ya jagoranci baje kolin kayayyakin Fasaha a daidai wannan lokaci na tunawa da shekaru talatin da daya da juyin juya halin Musulunci a Iran.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a Bangladesh ya jagoranci baje kolin kayayyakin Fasaha a daidai wannan lokaci na tunawa da shekaru talatin da daya da juyin juya halin Musulunci a Iran. A gurin wannan kasuwar baje kolin an samu halartar ministan al'adu da sadarwa na kasar Bangladesh Abu Kalam Azad da kuma jakadan kasar iran a wannan kasa.


536805