IQNA

Manbobin Hukumar Limamai Ta Pakistan Sun Ziyarci Ofishin Tabligi Na Musulunci

Bangaren siyasa da zamantakewa;manbobin majalisar limamai na kasar Pakistan sun ziyarci cibiyar yada al'adu da Musulunci ta Hauzar birnin Qum.
Daga birnin Qum ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna bayan ta nakalto daga bangaren hulda da jama'a na kasa da kasa a ofishin yada addinin Musulunci na Hauzar Birnin Qum ta watsa rahoton cewa: mutane talatin da daya daga cikin mambobin majalisar limaman kasar Pakistan sun ziyarci wannan ofishi tare da ganawa da shugabannin wannan ofishi inda aka yi masu bayani dalla-dalla kan irin ayyukan da ofishin ke gudanarwa.

536816