Bangaren kasa da kasa:an kawo karshen taron kasa da kasa kan addini a birnin Dubai.
Bayan ta nakalto daga jaridar Khaleej Times cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; an kawo karshen taron kasa da kasa kan harkokin addini a birnin Dubai kuma wannan taro a jiya ne aka kawo karshensa a wata babbar Otel da ke birnin na Dubai kuma masana da kwararru na hukumar da ke kula da harkokin addini da zamantakewa ta kasashe goma sha takwas na duniya suka halarci wannan taro.Shi dai wannan taro an shirya shi ne da zummar daukaka shirye-shirye da suka shafi addini kuma an gudanar da bincike kan wannan lamari a cikin wasu makaloli ashirin da biyu.
540236