IQNA

Jaddada hadin Kai A Tsakanin Bangarorin Musulmi A Trablus Na Labanon

Bangaren siyasa da zamantakewa; a jiya ne bangaren mambobin kungiyar tauhidi Islami a Labanon sun bukaci hada kan kungiyoyin musulmi a Trablus.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna daga kasar Labanon ta watsa rahoton cewa: Balal Sa'id Shaaban babban darektan kungiyar Tauhid islami da Umar Ayubi da sahib Sa'id Sha'aban da balal Barudi ,Sheik Alkara'a trablus ,Majid Darwish da sauran mambobin kungiyar sun bukaci sauran kungiyoyin musulmi da su hada kansu da bunkasa duk wani kokari na ciyar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin kasashen musulmi a yanki da ma duniya baki daya.

540027