IQNA

Za A Fara Ilmantar Da Matasa Tarihin Ma'aiki (SWA) A Katar

Bangaren kasa da kasa;Hadin guiwar kungiyoyin bada agaji a Katar sun shirya wani hora kan tarihin rayuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa.
Bayan ta nakalto daga jaridar kasar katar Alshark cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran ikna ta watsa rahoton cewa: Hadin guiwar kungiyoyin bada agaji a Katar sun shirya wani hora kan tarihin rayuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa. Har ila yau wannan hadin guiwar kungiyoyin zai kai wadannan matasa gurare da daman a ilimi da tarihi na Musulunci da kuma guraren addini da ibada a Makka kuma kimanin matasa sattin ne za a nunawa wadannan gurare da basu horo.

540765