Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Al'ittihad ta kasar Hadeddiyar daular larabawa ta watsa rahoton cewa: an isa ga matakin karshe na gasar karatun kur'ani na Ra'asul Keima a Hadeddiyar daular larabawa inda aka samu halartar mahardata saba'in da daya. Ya kara da cewa; Umar bin Abdul Aziz Kasim babban sakataren shirya wannan gasar ne ya yi bayani dalla-dalla kan yadda za a gudanar da wannan gasar amma bangaren maza.
540781