Banagaren siyasa da zamantakewa: Masallacin Alrahman da ke karkashin kulawar ofishin kula da addinin Musulunci a labanon an kaddamar da shi tare da gudanar da gagaramin buki a yankin Ra'asul Beirut a tare da halartar firaministan wannan kasa.
Daga Labanon ne cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Masallacin Alrahman da ke karkashin kulawar ofishin kula da addinin Musulunci a labanon an kaddamar da shi tare da gudanar da gagaramin buki a yankin Ra'asul Beirut a tare da halartar firaministan wannan kasa. Har ila yau bayan firaministan akwai manyan baki da malumai da wakilan majalisa da jami'an gwamnati da suka halarci wajen wannan bukin.