IQNA

A Wani taro A Beirut Za A Gudanar Da Bincike Kan Dangantakar yankuna da tauraro Da fikihu

Bangaren ilmi da bincike; a birnin Beirut na kasar Labanon ne masana da malummai za su gudanar da wani taro da zai yi bincike da nazari kan ilimin tauraro da fikihu da shari'a kan ilimin tauraro da lokuttan sallah.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga reshenta na Labanon ta watsa rahoton cewa: a birnin Beirut na kasar Labanon ne masana da malummai za su gudanar da wani taro da zai yi bincike da nazari kan ilimin tauraro da fikihu da shari'a kan ilimin tauraro da lokuttan sallah. Shi dai wannan taro a ranekun alhamis da juma'a biyar zuwa shidda ga watan Isfan za a gudanar da shi karkashin sa idon Allama Faddullah marji'in yan shi'ar kasar Labanon.


541021