Bayan ta nakalto daga bangaren hulda da jama'a na hukumar kara kusanci a tsakanin mazhabobi na Musulunci ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Hukumar dake kula da kara kusanci a tsakanin mazhabobi da ken an birnin Tehran ta bada labarin cewa; za a gudanar da taron makon hadin kan musulmi karo na ashirin da uku. A duk shekara a nan birnin Tehran ana gudanar da taro kan hadin kan musulmin duniya inda malummai dam asana suke tattauna hanyoyin kara hadin kai a tsakanin musulmi da kuma irin matsalolin da ke addabarsu a fadin duniya da yadda za su warware su da magance su.
541002