Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: tare da tuntubar juna a tsakanin komitin musulmi na kasar Zimbabwe a masallatan garuruwan Kaduma da Mautara da Harare za a raya daren maulidin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi .Har ila yau bukukuwan bukin maulidin ma'aikin Allah (SWA) za a samu halartar Irakniyawa da ke zaune a wannan kasa ta Zimbabwe kuma a ranar alhamis mai zuwa ne za a gudanar da wannan buki.
542589