Bayan ta nakalto daga jaridar aldastur da ke fitowa a kasar Jodan cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: a hukumce kakakin gwamnatin Jodan y ace wani sabon makirci ne na yahuda na kokarin mamaye kabarin Bilal bin Rabah da masallacin annabi Ibrahima (AS). A mamayen da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take yin a ganin ta karbe gurare masu muhimmanci na tarihi a duniyar musulmi a yankin Palasdinu ta kawar da kai da duk wata doka da ta shafi kasa da kasa tare da fitpo da wani sabon salon a mamaye kabarin sahabin Annabi Muhammd tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa Bilal bin Rabah da kuma masallacin annabi Ibrahima (AS).543054