Bangaren al'adu da fasaha; ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Indiya ya bayyana cewa iran aa shirye take ta fadada dangantakarta da kasar Indiya ta fuskar cibiyoyin ilimi da na addini.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna ta watsa rahoton cewa: ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Indiya ya bayyana cewa iran aa shirye take ta fadada dangantakarta da kasar Indiya ta fuskar cibiyoyin ilimi da na addini. A wata ganawa ce da Baha'ul Din Muhammad Nadwi shugaban jami'ar Musulunci ta Darul Hindi Karim Najafi mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar ta Indiya ya bayyana shirin Iran na fadada dangantaka da kasar indiya ta dukan bangarori na ilimi da al'adu.
542905