Bangaren al'adu da fasaha: Ofishin da ke kula da harkokin yada al'adun Iran a kasar Seraleyon ta bada labarin gudanar da taron maulidi na zagayowar irin wannan rana ta haifuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Ofishin da ke kula da harkokin yada al'adun Iran a kasar Seraleyon ta bada labarin gudanar da taron maulidi na zagayowar irin wannan rana ta haifuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa. Kuma a dabra da wannan buki na maulidin ma'aikin Allah (SWA) akwai na tunawa da irin wannan rana ta haifuwar jikan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa wato Imam Sdaik (AS).
543835