IQNA

A Zimbabwe Za A Gudanar Da Bukin farkon Wilayar Imam Mahdi (AS)

Bangaren ilimi da bincike" a kasar Zimbabwe za a gudanar da bukin tunawa da zagayowar farkon fara wilayar Imam Mahdi (AS).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; a kasar Zimbabwe za a gudanar da bukin tunawa da zagayowar farkon fara wilayar Imam Mahdi (AS). Wannan buki za a gudanar da shi ne tare da halartar yan Shi'a daga kasar Labano ,Yan shi'a daga Iran da kuma wasu yan shi'ar a kasar ta Zimbabwe da ma'aikatan ofishin jakadancin jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Zimbabwe kuma wannan da zummar nuna farin ciki da wannan rana ta matsayin Imami da wilaya ta Hadarat Imam Mahdi (AJ) da kuma bayyana al'ada ta mahdawiya gay an shi'a da matasan wannan kasa.

543725