Daga kasar Suriya ne bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta al'jazira cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna ta watsa rahoton cewa; shugaban kasar Suriya Bashar Al'asad ya bukaci kasashen larabawa da mataki na kasa da kasa da su kara kaimi da kokarin da zai kawo karshen killacewar da ake yi wa al'ummar yankin Gaza. Yankin Zirin Gaza tun kafin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai masa harin ta'addanci na kwanaki ashirin da biyu yana killace kuma bayan wannan harin ta'addanci ya ci gaba da zama a killace.
543696